6 Satumba 2020 - 10:12
​An Kama Wata Tawagar Yan Ta’adda Ta Kungiyar Daesh A Kasar Lebanon

Majiyar sojojin kasar Lebanon ta ba da sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar kama tawagogin mayakan kungiyar Deash 2 a kasar.

ABNA24 : Shafin yanar gizo na Al-Ahad na kuma labarai, na kasar ta Lebanon ya nakalto babban kwamandan sojojin kasar ya na fadar haka a jiya Asabar.

Babban kwamandan ya kuma kara da cewa an kama ‘yan ta’addan na kungiyar Daesh ne a lokacinda su ke shirin kai wasu hare-haren ta’addanci a cikin kasar.

Amma jami’an tsaron kasar su ka sami sa’ar kamasu kafin su kai hare-haren.

Labarin ya kara da cewa an kama gungu ‘yan ta’addan ne a warare biyu na kasar wato yankin Bikaa da kuma arewacin kasar.

Daga karshe labarin ya kammala da cewa ‘yan ta’addan sun sami horon soja mai yawa, sannan an gano makamai masu yawa a hannunsu. (19)

342/